- 20 minutes 36 secondsFaɗa ya sake ɓarkewa tsakanin Amurka da Iran bayan rugujewar yarjejeniya
Shirin a wannan makon zai leka Gabas ta Tsakiya inda rikici ya sake barkewa tsakanin Amurka da Iran abin da ya kawo karshen yarjejeniyar fahimtar juna ta watanni uku da suka cimma a tsakaninsu. Bayan nan, shirin zai taɓo wasu mahimman lammuran da suka wakana a sassan yammacin nahiyar Afirka, musamman Najeriya, Nijar da Kamaru.
11 July 2026, 6:30 am - 19 minutes 19 secondsBitar muhimman labarun da suka faru a mako daga Rfi hausa
Ƙungiyar kare hakin bil Adam Amnesty International ta zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu da gaza kare ƴan Najeriya daga matsalolin ta’addanci da na tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya.........
4 July 2026, 6:38 am - 20 minutes 36 secondsAna ci gaba da laluben dubban mutanen da suka ɓata a girgizar kasa a Venezuela
Shirin na wannan mako zai soma ne daga Venezuela inda a yammacin ranar laraba girgiza ƙasa mai karfin maki 7 a ma’aunin celcius ta afkawa arewa maso yammacin ƙasar abin da ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali da alhini sakamakon rasa rayuka da dukiyoyi.
Alkaluman hukumomi sun ce sama da mutum 900 ne suka rasayukansu kawo yanzu yayin da sama da 4,000 suka jikkata bayaga sama da 50,000 da suka yi ɓatan dabo.
Tuni dai Ƙasashe suka fara aike da saƙonni jaje baya ga jami’an agaji don taimakawa a aikin laluben mutanen da girgizar ƙasa ta birne da kuma waɗanda ke cikin mawuyacin hali.
A nahiyar Turai kuwa matsanancin zafi ya tilasta dakatar da harakokin yau da kullum a ƙasashe da dama.
A wasu birane zafin ya kusa kai maki 40 a ma’aunin Celsuis abin da ya tilsatawa mahukunta fitar da gargaɗi da dakatar da muhimman harakokin yau da kullum.
A Faransa, an rufe ɗaruruwan makarantu a ranar Litinin yayin da aka rage lokacin tashin wasu dubbai.
A wani labarin kuma, ranar Alhamis da ta gabata al’ummar musulmi mabiya ɗarikar Shi’a a duniya suka gudanar da juyayin tunawa da kisan jikan Annabi Muhammad SAW, da aka yi a garin Karbala na ƙasar Iraqi ta yanzu, kwanakin da ke yiwa laƙabi da Tasu’a da Ashura.
A ƙasar Iran wadda itace cibiyar mabiya Shi’a a duniya an gudanar da bikin na wannan rana a cikin yaƙi da kuma rashin jagoran addinin ƙasar Ayatoullah Ali Khamna’ei, wanda ke jagorantar ranakun a kowacce shekara.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Oumarou Sani.
27 June 2026, 9:06 am - 20 minutes 58 secondsShirin yayi bita kan harin da aka kai filin jirgin saman Yamai da ma wasu labarai
Shirin na wannan mako ya mayar da hankali kan bitar muhimman labaran da suka faru a sassan duniya cikin makon da muke bankwana da shi.
Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sanni.
20 June 2026, 9:43 am - 20 minutes 13 secondsShirin ya fara da yadda aka buɗe bikin gasar cin kofin duniya a ƙasar Mexico
Ranar Alhamis 11 ga wannan watan aka yi bikin buɗe gasar cin kofin duniya karo na 23, gasar da itace karo na farko da ƙasashe 3, Amurka da Canada da kuma Mexico su ka karbi baƙunci, sai dai kuma an gudanar da zanga-zanga a wasu sassa na birnin ƙasar.
Ƙasashe 48 ne ke fafata domin samun zakaran bana kuma yan wasa 1,248 da alkalan wasa 52 za su jagoranci wasanni 104 da za'a kwashe kwanaki 39 ana yi.
A cikin shirin akwai labarin, shugaban Amurka Donald Trump, da ya ce ya soke shirinsa na kai munanan hare-haren da ya shirya yi a Iran, sakamakon wata tattaunawar da yace ya yi da wasu ƙusosshin gwamnatin ƙasar, Ikrarin da ya zuwa yanzu hukumomin ƙasar basu ce komai akai ba.
Haka zalika, Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da dokar kafa ƴansandan jihohi da gagarumar rinjaye, matakin da zai bai wa gwamnatocin jihohi damar kafa rundunar da za ta taimaka wajen magance matsalolin tsaron da suka addabi ƙasar.
A Jamhuriyar Nijar gwamnati ce ta rattaɓa hannu a kan dokar haramta auran jinsi ko kuma mu’amalar jinsi guda wanda ta tanadi hukuncin ɗaurin da ka iya kai wa shekaru 20 a kan duk wanda aka samu da laifin yin haka.
A wani abu da ba’a saba gani ba, Kungiyar mayaƙan JNIM mai alaƙa da Al Qaeda reshen Mali ta yi tayin bayar da tukwicin miliyoyin Yuro ga duk wanda ya ba ta bayanai kan inda shugaban kasar Assimi Goita da manyan jami'an sojinsa suke, a yayin da ta bayyana gwamnatin a matsayin haramtacciyar.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin, tare da Oumarou Sani.
13 June 2026, 10:02 am - 20 minutes 47 secondsYadda malaman makaranta suka gudanar da zanga-zanga kan rashin tsaro a Najeriya
Shirin na wannan mako ya waiwaya halin da duniya ke ciki a fannin tsaro, rikice-rikice da kuma Diflomasiyya
6 June 2026, 10:11 am - 20 minutes 57 secondsMahajjata kusan miliyan biyu sun gudanar da aikin Hajjin bana
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Oumarou Sani, kamaar yadda aka saba ya yi bitar wasu daga cikin muhimman lamurran da suka wakana a makon da muka yi wa bankwana.
Daga cikin muhimman batutuwan kuma akwai, yadda Musulmi kusan miliyan biyu suka samu nasarar gudanar da aikin Hajjin bana.
Shirin ya kuma leƙa Yankin Gabas ta Tsakiya domin jin halin da ake ciki, musamman kan ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Iran.
30 May 2026, 6:35 am - 20 minutes 26 secondsRFI Hausa ta cika shekaru 19 da fara watsa labarai cikin harsshen Hausa
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya fara ne da labarin cikar wannan tasha ta RFI Hausa shekaru 19 da kafuwa.
Ranar alhamis 21 ga wannan watan gidan Rediyonku na RFI sashen Hausa ya cika shekara daya- daya har 19 da soma yada shirye-shiryensa .
A shekara 2007 ne kwarrariyar ƴar Jarida Lanni Smith ta kirkiri sashen Hausa na RFI da aka yi wa matsuguni a birnin Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Kuma bikin na bana yazo a wani yanayi da kafar ke kara samun daukaka a idon duniya.
23 May 2026, 6:21 am - 21 minutes 4 secondsYadda harin dakarun Najeriya ya kashe ɗimbin mutane a kasuwar Zurmi
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' yana bita ne na mahimman labaran al'amura da suka wakana a makon da ya gabata. a wannan makon shirin ya soma ne daga Najeriya inda a farkon makon da ya wuce wani harin da dakarun Najeriya suka kai ta sama a kasuwar Tumfa ta karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamafara ya hallaka akalla mutum dari 100 tare da jikkata wasu da dama.
Wannan harin da ke zaman mafi muni da dakarun kasar su kai kan fararen hula shi ne na uku a cikin kasa da wata guda .
16 May 2026, 8:32 am - 18 minutes 46 secondsWasu daga cikin muhimman labaru a cikin makon daya gabata
A wannan mako shirin zai mayar da hankali akan batun zabukan fidda gwani na Jam'iyar APC mai mulki a Najeriya da kuma rikicin cikin gida a sauran jam'iyun ƙasar suka ɗauki hankulan al'uma.
9 May 2026, 5:56 pm - 20 minutes 45 secondsYadda haɗakar ƙungiyoyi suka ƙaddamar da farmaki a sassan Mali
Shirin ya soma daga ƙasar Mali inda a ranar 25 ga watan Afrilun da mu kayi ban kwana haɗakar mayakan Abzinawa na FLA da na ƙungiya masu ikirarin jihadi ta JNIM suka ƙaddamar da mugayen hare-hare a garuruwa huɗu na ƙasar da suka haɗa da Sevare, Kidal, Gao da kuma Kati.
A garin Kati da ke zaman babban sansanin sojin ƙasar ƴan bindigar sun yi amfani da motoci shake da bama-bamai da manyan bindigogi inda suka kai hari kan gidan ministan tsaron kasar Sadio Camara tare da hallaka shi.
A kasar Chadi kuwa aƙalla mutum 42 ne suka mutu bayan ɓarkewar wani rikicin ƙabilanci da ya faro sanadiyyar taƙaddama tsakanin wasu mata biyu yayin da suke ɗiban ruwa a wata rijiyar bayan gari.
A Najeriya kuwa, ranar Alhamis ne kotun ƙolin ƙasar ta yanke hukunci kan rikicin cikin gida na jam'iyyun ADC da PDP.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin, tare da Oumarou Sani.
2 May 2026, 8:32 am - More Episodes? Get the App